Alhamis a Iran, mutane goma sha daya ne kasar ta aiwatarda hukuncin kisa ta rataya akansu, a birane da dama, biyar daga cikinsu an aiwatarda hukuncin a bainar jama’a.
Kamfanin dillancin labaran kasar (IRNA) a takaice, yace mutanen an samesu da laifuffuka da suka kama daga kisa da safarar miyagun kwayoyi.
Wadanda aka ratayesu a bainar jama’an, sun hada da wani da ya kashe mata biyar a birnin Qazvin, dake yammacin Tehran. Saura hudu da suka fuskanci hukuncinsu a bainar jama’a a birnin Shiraz, laifuffukansu sun hada da fashi da makami da kuma satar mutane.
Farisa tana amfani da tsarin shari’ar Islama, inda wasu laifuffuka masu tsanani suke samun hukuncin kisa.
Kungiyoyin rajin kare hakkin bil Adama, suna zargin Iran ce ta biyu bayan China a yawan mutane da suke fuskantar hukuncin kisa. Farisa tayi watsi da zargin tsarin shari’arta.