Shugaba Boris Tadic na kasar Serbia ya bada sanarwar cewa karshenta dai an cafke Ratko Mladic, tsohon kwamnadan dakarun Bosniyawa a lokacin kazamin yakin da aka yi jim kadan bayanda tsohuwar kasar Yugoslavia ta wargaje.
Shugaba Tadic yace a cikin Serbia aka kama Mladic kuma har an soma daukan matakan hannunta shi fa kotun karrarakin yake-yake ta Majalisar Dinkin Duniya. Shugaban na Serbia yace zasu gudanarda binciken gano dalilin da yassa aka share shekaru 16 kafin a cafke wannan tsohon madugun ‘yantawayen na Bosnia, Mr. Mladic,dan shekarun haifuwa 69. Daman tun bayau ba ita wannan kotun yake-yaken ta duniya ta tuhumci Mladic da laifukkan azabatarwa da kashekashen gillar da aka tapka a lokacinda mayakansa suka kama birnin Sarajevo, lokacinda ya jagoranci hallaka al’ummar Musulmin Bosnia sunfi dubu 8, kusan dukkansu maza da yara ‘yanmaza, a kusa da garin Srebrenica.
Ana daukar kisan gillar da aka yi a Srebrenica a matsayin ta’asa mafi muni da aka taba yi a duk Turai tun bayan yakin duniya na biyu. Haka kuma Mladic ne aka ce yayi jagorancin fattakkar wattani 43 da aka yi wa Sarajevo, babban birnin na Bosnia, daga 1992-1996, wanda aka ce itace kawanya mafi tsawo da aka taba yi wa duk wani birni a duk tarihin yake-yake na duniya.
Shi dai Mladic daman daya ne daga cikin mutane ukku da aka dade ana nema don rawar da suka taka a yakin na Bosnia. A 2008 aka kama na biyun, Radovan Karadzic, yayinda har yanzu ake farautan na ukku, Goran Hadzic, wani kusar Sa rbiyawan Croatia.