Ministan Shari'ar Amurka Ya Nemi Hukumcin Kisa Wa Masu Safarar Miyagun Kwayoyi

Atoni Janar kuma Ministan Shari'ar Amurka Jeff Sessions

Biyo bayan furucin da Shugaban Amurka ya yi na cewa zai yaki masu sayar da, da kuma yin ta'ammali da miyagun kwayoyi, ministan shari'a ya umurci lauyoyin gwamnayi 93 su nemi hukumcin kisa wa duk wanda aka gurfanar dashi gaban kuliya akan laifin da suka jibanci miyagun kwayoyi

Ministan Shari’a kuma Atoni janar na Amurka Jeff Sessions ya bukaci masu gabatar da kara na gwamnatin tarayya da su bukaci hukuncin kisa akan wasu shari'u masu alaka da madugun miyagun kwayoyi. Jeff dai yana jaddada goyon bayansa ne ga shawarar da shugaba Donald Trump ya bayar game da yaki da mummunar bala'in shaye shayen miyagun kwayoyi data addabi kasar ahalin yanzu.

A cikin wata wasika ko shawarwari da ya aikewa lauyoyin gwamnatin tarayya su 93 a duk fadin kasar, Sessions ya ce tilas ne su duba duk wata damar da suke da ita na ganin an shawo kan wannan matsalar shaye-shayen kwayoyi, ciki ko harda duba yiwuwar anfani da hukunci kisa idan yin hakan ya dace.