Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bam Ya Sake Fashewa A Jihar Texas Ta Nan Amurka


Jami'an FBI suna binciken lamarin har sai sun kai ga kama wani ko wasu
Jami'an FBI suna binciken lamarin har sai sun kai ga kama wani ko wasu

A karo na shida wani bam ya sake fashewa a wurin tantance kunshe kunshen sakaonnin kamfanin Federal Express, kafin wannan wani ya fashe a wani shago dake sayar da kaya araha domin taimakawa marasa karfi

Rahotanni daga Jihar Texas a nan Amurka sun ce 'Yansanda a birnin Austin sun garzaya inda wani bam ya tashi a wani kantin sayar da kayayyaki da rahusa da zummar taimakawa marasa karfi da ake kira Goodwill.

Jami'an kiwon lafiya sun ce an kai mutum daya asibiti, "raunukan da yaji suna da tsanani" amma ba'a jin hakan zai kai shi ga rasa ransa."

Wannan shine karo na shida da ake fuskantar irin wadannan fashe fashen bama=bamai cikin mako uku da suka wuce,mutane biyu sun halaka sakamakon wadannan hare haren, da jikkata wasu hudu sosai.

A daren Litinin, wani kunshi da aka aika ta kamfanin Federeal Express, ya fashe a wani wurin tara sakonnin kusa da birnin San Antonio, mai tazarar kilomita 96 daga Austin. Babu wanda ya jikkata a wannan fashewar.

Kunshin ya fashe ne akan rariyar da take tantance sakonni. Rahotanni sun ce kunshin an aika shi zuwa birnin na Austin ne.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG