Ministan ya ce rikicin dai ya samo asali ne sakamakon wani hadari da ya rutsa da wasu yan Achaba inda wata mata ta fado daga kan Babur abin yazo da karar kwana kuma wata mota ta take kan matar ta rasu.
Sai 'yan uwan matar suka kone babur din yayinda su ma 'yan Achaban suka shiga kasuwar 'yan katako inda Galibi 'yan kabilar Igbo ne suka fara kone shaguna da motoci.
Ministan yace rikicin ko kadan bai da alaka da Addini ko kabilanci, amma dai aika aika ne kurum na 'yan kwaya da 'yan wiwi dake amfani da irin wannan dama don haddasa rudani.
A saboda haka, ministan ya bada umarnin kaddamar da bincike musamman ma ganin an kashe mutane biyar kuma anyi amfani da bindiga, inda ya bukaci a bincika wace irin bindiga .
Daga nan Ministan ya bada umarnin rufe kasuwanni uku dake yankin har sai abinda hali yayi, inda yace za a sake fasalta kasuwannin baki daya.
Itama rundunar 'Yan sandan Abujan ta yi kira ga jama'ar birnin da suyi taka tsantsan wajen sha'anin tsaro kuma an kara yawan jami'an tsaron 'yan sanda da sojoji da sauran jami'an tsaro da su ke cikin shirin ko ta kwana.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5