Miliyoyin Amurkawa ne za su zauna a gaban akwatunan talabijin dinsu don kallon muhawarar Mataimakiyar Shugaban Amurka Kamala Harris ta jam’iyyar Democrat da abokin hamayyata na Republican tsohon Shugaban Amurka Donald Trump.
A wannan Talata za a fafata a muhawarar watanni biyu bayan muhawarar da aka yi tsakanin Trump da Shugaba Joe Biden – kafin ya janye takararsa ya mika ragama ga Harris.
Kiyasi ya nuna mutum miliyan 51.3 ne suka kalli muhawarar Trump da Biden a watan Yuni.
Ana kuma hasashen wadanda za su kalli wannan muhawara wacce za a yi a birnin Philadelphia na jihar Pennsylvania za su haura hakan duba da shaukin da jama’a ke nuna.
Kamala Harris da Donald Trump suna shiri daban-daban game da muhawarar neman shugabancin kasar, wanda ke nuna bambance-bambancen hangen nesansu ga kasar, da kuma yadda suke kimtsawa muhawarar.
Harris ta shafe karshen mako a kulle a wani tsohon otel a tsakiyar garin Pittsburgh, inda ta mai da hankali kan inganta yadda za ta ba da amsa cikin tsawon minti biyu kamar yadda ka'idodin muhawarar suka tanada.
A gefe guda kuma, Trump ya yi watsi da muhimmancin yin nazari don muhawarar a fili. Tsohon shugaban kasar ya zaɓbi cike kwanakinsa da ayyukan da suka shafi kamfen maimakon yin nazari.
Gidan talabijin na ABC ne zai jagoranci muhawarar.