Mike John Ya Sake Lashe Kujerar Kakakin Majalisar Wakilan Amurka

Mike Johnson

Johnson ya samu kuri’u 218 yayin da 215 suka nuna adawa.

Dan Republican Mike Johnson ya lashe zaben sake zama Kakakin Majalisar Wakilai a wani zaben da ya kasance mai cike da rudani a kuri’a ta farko, duk da turjiya daga wasu ‘yan jam’iyyar GOP masu tsattsauran ra’ayi.

Bayan karbar sandar jagoranci, Johnson ya yi alkawarin rage girma da ikon gwamnatin tarayya.

Wannan yanayi mai cike da rashin tabbas na nuni ga irin kalubalen da ke gaban sabuwar Majalisar Dokoki kafin Shugaba mai jiran gado Donald Trump ya dawo Fadar White House tare da cikakken ikon jam’iyyar ta Republican a Washington.

A karshe dai, Johnson ya samu nasarar shawo kan ‘yan adawa biyu da suka sauya ra’ayinsu suka ba shi goyon baya, yayin da Trump ya kira ‘yan majalisar Republican da suka yi adawa da shi daga filin wasan golf.

Johnson ya samu kuri’u 218 yayin da 215 suka nuna adawa.