Tun daga karfe 12 ranar 3 ga watan Janairun da muke ciki agogon Amurka, sabuwar Majalisar Dokokin kasar za ta fara gudanar da ayyukanta da gabatar da jerin wasu tsare-tsare a Majalisar Wakilai.
Da farko za'a fara zaben sabon kakaki, inda mutumin da ke kan kujerar Mike Johnson, ke fafutukar ci gaba da zama a kanta.
Babban kalubale ga Johnson shine zai bukaci kusan dukkanin kuri'un 'ya'yan jam'iyyar Republican da ke majalisar domin sake zama kakakin.
Sa'ar da Johnson ke da ita, ita ce zababben shugaban kasa Donald Trump na goyon bayan takararsa.
Dandalin Mu Tattauna