FIFA Ta Kuma Tabbatar Da Messi Zakaran Kwallon Duniya Na Shekarar 2022

The Best FIFA Football Awards

Dan wasan gaban Argentina da Paris St-Germain, Lionel Messi, shi ne aka zaba gwarzon dan wasan kwallon kafa na shekara a gasar FIFA na 2022.

Messi da ya lashe madaukakiyar kyautar Ballon d’Or sau bakwai ya doke dan wasan gaban Faransa Kylian Mbappe da Karim Benzema a kyautar.

Messi, mai shekaru 35, ya taimakawa Argentina lashe gasar cin kofin duniya da aka yi a Qatar a shekarar 2022, da kuma ya zura kwallaye 27 a wasanni 49 da ya buga wa kulob da kasar a 2021-22.

The Best FIFA Football Awards

'Yar wasan Barcelona, Alexia Putellas ta zama fitacciyar 'yar wasan mata ta bana.

A bikin da aka yi a birnin Paris, Lionel Scaloni, wanda ya jagoranci Argentina ta lashe gasar cin kofin duniya karo na uku, ya zama gwarzon kocin maza na bana.

Scaloni ya doke Pep Guardiola - wanda ya jagoranci Manchester City lashe gasar Premier karo na shida - da kuma kocin Real Madrid Carlo Ancelotti wanda ya lashe gasar zakarun Turai.

FIFA World Cup Qatar 2022 - Group C - Poland v Argentina

Kocin Ingila Sarina Wiegman ta samu kyautar gwarzon kocin mata ta bana bayan da ta jagoranci kungiyar Lionesses zuwa ga cin kofin Turai a gida a bara, babban kofin farko na kungiyar.

An tbbatar da golan Aston Villa da Argentina Emiliano Martinez a matsayin babban mai tsaron ragar maza.

Benfica's Enzo Perez, left, from Argentina, challenges Fenerbahce's goalkeeper Volkan Demirel, right, and Cristian, from Brazil, during their Europa League semi final second leg soccer match in Lisbon, Thursday, May 2, 2013.

Dan wasan mai shekaru 30, ya taimaka wa kasarsa ta lashe gasar cin kofin duniya, inda ya tare fanareti hudu a yayin gasar, ciki har da bugun daga kai sai mai tsaron gida da Argentina ta doke Faransa a wasan karshe.

Dan wasan kwallon masu nakasa Marcin Oleksy na kungiyar Warta Poznan ta kasar Poland ya lashe kyautar Fifa Puskas ta gwarzon wanda ya zura kwallo mafi kyau da ya ci Stal Rzeszow, lokacin da ya aike da wata kwallo mai karfin gaske zuwa cikin raga tare da taimakon ‘yan wasansa.