Messi Ya Ci Kwallonsa Ta Farko A PSG

Lionel Messi, hagu, yana murnar zura kwallonsa ta farko tare da Neymar, dama (Hoto: AP)

Messi ya ci kwallon ce a minti na 74 bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci a wasan wanda ya City ta rika rutsa PSG.

Lionel Messi ya ci wa sabuwar kungiyarsa ta Paris Saint Germain (PSG) kwallonsa ta farko tun bayan da ya koma buga kwallo a Faransa.

A watan Agusta Messi ya koma PSG daga Barcelona, bayan da aka samu akasin sabunta kwantiraginsa a gasar ta Sifaniya, wacce anan ya kwashe iya rayuwarsa yana taka kwallo kafin komawa PSG.

An yi ta yamadidi kan gaza zura kwallo da Messi ya yi, tun bayan komawarsa Paris, inda masu bibiyar kwallon kafa suka rika kwatanta shi da ‘yan wasa irinsu Ronaldo (Manchester United) da Lukaka (Chelsea) da tuni suka fara ruwan kwallaye tun bayan da aka fara wannan kakar wasa.

Sai dai a karon faro, Messi ya wuce fushinsa akan Manchester City a haduwar da suka yi a Paris a gasar cin kofin zakarun nahiyar turai ta Champions League.

Messi ya ci kwallonsa ne a minti na 74 bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci a wasan wanda ya City ta rika rutsa PSG.

An tashi a wasan da ci 2-0.

Dan asalin Argetina, Messi mai shekara 34, ya bugawa PSG wasa uku ba tare da samun nasarar cin kwallo ba.

Masu sharhi sun yi ta nuni da cewa Messi bai saba da salon taka leda a Faransa shi ya sa ya yi jinkirin zura kwallo yayin da wasu ke ganin lokaci ne kawai bai yi ba.

Idrissa Gueye ne ya fara zura kwallon farko a ragar City a minti na 8 da fara wasa.