Lionel Messi ya buga wasansa na farko a sabuwar kungiyarsa ta Paris Saint-Germain wacce ta kara da Reims.
PSG ta doke Reims da ci 2-0, kuma Kylian Mbappe ne ya zura duka kwallayen biyu.
Messi ya shiga wasan ne a minti na 66 inda ya canji Neymar, wanda sun taba buga wasa tare a Barcelona a gasar La Liga.
‘Yan wasan biyu sun rungumi juna a lokacin da aka zo yin canjin.
Bayan shekaru da ya kwashe yana murza leda a Barcelona, Messi wanda ya taba lashe kyautar zakaran dan kwallon duniya ta Ballon d’Or sau shida ya kuma daga kofin zakarun nahiyar turai sau hudu, ya buga wasansa na farko a kungiyar inda ya shiga bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.
A filin wasa na Barcelona na Camp Nou, Messi ya saba taka leda a gaban ‘yan kallo dubu 99,000, amma a filin wasan PSG na Stade Auguste Delaune mai cin ‘yan kallo dubu 20,000 dan wasan na Argentina ya bude babin kwallonsa a gasar ta Ligue 1 a Faransa.
Makonni uku da suka wuce Messi ya koma PSG daga Barcelona bayan da kungiyar ta Sifaniya ta gaza sabunta kwantiraginsa.
Duk da cewa ana alakanta shi da kokarin komawa kungiyar Real Madrid PSG ta saka Mbappe a wasan.
Mbappe ya zura kwallayensa ne tun kafin Messi ya shiga wasan.
A karon farko, Messi ya nuna sabuwar rigar wasan kwallonsa ta PSG