Dan wasan Najeriya kuma zakaran kugniyar Napoli Victor Osimhen ya shiga tsaka mai wuya bayan da aka rufe kasuwar cinikin ‘yan wasa ba tare da ya samu kungiya ba.
Osimhen wanda ya yi yunkurin barin kungiyarsa ta Napoli, ya gaza cimma matsaya da kungiyar Chelsea da ke Ingila da Al Ahli ta kasar Saudiyya bayan da aka rufe kasuwar cinkiyyar ‘yan wasan a ranar Juma’a 30 ga watan Oktoba.
Rahotannin sun ce tuni har Napoli ta cire sunan Osimhen daga jerin tawagar ‘yan wasanta na farko a karkar wasa ta bana.
A wani abu da ake ganin mataki ne na maye gurbin Osimhen, a makon da ya gabata Napoli mai buga wasannin a gasar Serie A ta kasar Italiya ta kammala sayen dan wasan Belgium Romelu Lukaku.
Rahotanni sun ce Osimhen ya ki amincewa da tayin da Chelsea ta yi na pam miliyan 4 a daukacin kakar wasan, kudin da ya gaza matuka da pam miliyan 10 da Napoli take biyansa.
A Al Ahli kuwa, Osimhen ya amince da tayin pam miliyan 30 a daukacin kakar wasan, sai dai Napoli ta nemi karin pam miliyan 5 a matsayin kudaden alawus, lamarin da ya ruguza cinikin.
Yanzu Osimhen ya makale a Napoli wacce ta cire shi a jerin 'yan wasanta na farko, ana kuma tunanin dangantakarsa da manojojin kungiyar za ta raunana.
A halin yanzu sai a watan Janairu za a sake bude kasuwar cinikayyar 'yan wasan.