Mataimakiyar sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Amina Mohammed ce ta bayyana hakan yayin wani taro na ganin yadda za a dama da mata a aikin soja.
Mataimakiyar jagoran majalisar dinkin duniyar ta ce suna yabawa gwamnatin Najeriya wajen karfafawa mata gwiwa su ke shiga aikin soja.
Najeriya a cewarta, kamar sauran kasashe, na fama da kalubalen tsaro iri-iri da kuma a cikinsa galibi mata da kananan yara ne su ka fi dandana kudar su.
Don haka sojojin Najeriya na da gagarumar rawar da za su taka don maganin aukuwar ricici da ma kawo karshensa idan ya faru.
Taron dai da hedkwatar tsaron Najeriya ta shirya da nufin inganta tare da karfafa rawar da mata ke takawa a gidan soja ya sami halartar manyan baki da dama.
Babban hafsan tsaron kasar, Janaral Christopher Musa ya yi bayanin cewa jigon taron shi ne gina hanyar shigo da mata cikin shawo kan matsalolin tsaro, an yi hakan ne da nufin fuskantar hakikanin abin da ke akwai wajen damawa da jinsin mata da su ne su ka fi yawa.
Hakan a cewar Janar CG Musa zai baiwa rundunar sojin damar tsarawa, aiwatarwa, sa ido da kuma harsashen irin hobbasan da mata ke iya yi a fagen daga da ma bangaren gudanarwa da hakan ka iya karfafa rawar da matan ke takawa wajen shawo kan matsalar tsaro a kasar.
Saurari rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5