Mambobin kwamitin su 15 suka nuna amincewarsu ta bai-daya a jiya Talata,inda suka nuna fushinsu kan yadda bangaroroin da ke fada a kasar suka yi bris da bukatan da Majalisar Dinkin Duniya ta gabatar game da yakin na Syria da ke kara kazancewa.
Wannan kira na kwamitin, an yi shi ne domin gwamnatin Syria da kungiyar IS da Al- Nusra Front da kuma da kuma mayakan da ke da alaka da kungiyar Al Qaeda.
Har ila kwamitin sulhun, ya yi Allah wadai da ayyukan azabtarwa da kisa da kuma batan mutane da sauran laifukan yaki da ake zargi na faruwa a kasar, ciki har da na cin zarafin kananan yara.
A farkon jiya Talata, shugaban Majalisar Dinkin Duniya a ofishin Majalisar da ke Geneva, Michael Moller, ya ce za a yi wani zama domin tattauna rikicin Syrian a wata mai zuwa, ba tare da ya ambaci takamaimain ranar da za yi zaman ba.
Amma ya ce mai yuwuwa a yi zaman a karshen watan Janairu mai kamawa.