MDD Ta Amince Da Kare Falasdinawa Fafaren Hula Dake Karkashin Mamayar Yahudawa

Jakadan Falasdinawa Riyad Mansour a Majalisar Dinkin Duniya, MDD, yayinda yake jawabi

Bayan kai komo da aka yi a Majalisar Dinkin Duniya, MDD, kasashe 120 sun amince da kare Falasdinawa dake wuraren da Yahudawa suka mamaye yayinda wasu 45 suka karacewa kudurin kana wasu 8 suka nuna adawarsu

Majalisar Dinkin Duniya ta amince da wata matsaya da ta cimma a jiya Laraba, wacce ta yi kira da a samarwa Falasdinawa fararen hula kariya, - wadanda suke zaune a karkashin yankunan da Yahudawa suka mamaye.

Wannan kira na zuwa ne, bayan da Amurka ta dakile wani yunkuri makamancin wannan a kwamitin sulhu na majalisar.

Bayan kai ruwa rana da aka yi, inda wani kuduri da Amurka ta gabatar wanda ke Allah wadai da kungiyar Hamas ta Falasdinawa ya gaza shiga cikin kudurin, an amince da ainihin kudurin da kuri’u 120 yayin da mambobin 8 suka nuna adawarsu, sannan wasu mambobi 45 suka kaurcewa kada kuri’a.

Kudurin dai bai ambaci kungiyar Hamas karara ba, amma kuma ya yi Allah wadai da “duk ayyukan gallazawa fararen hula, kama abin da ya hada da ayyukan ta’addanci da na tunzura jama’a da kuma lalata dukiya.

Kudirin har ila yau, ya yi tir da duk wani yunkuri na amfani da karfin da ya wuce kima, tare da nuna banbanci da dakarun Isra’ila ke yi akan Falasdinawa.