MDD: Kwamitin Sulhu Ya Amince da Yarjejeniyar Kafa Gwamnatin Hadaka a Libya

Taron Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya (MDD)

Ba tare da wata gaddama ba a Majalisar Dinkin Duniya kwamitin sulhu ya amince da kafa gwamnatin hadin kai kamar yadda bangarorin dake rikici da juna suka yadda su yi.

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya baki daya ya amince da yarjejeniyar kafa gwamnatin hada kan kasa,kamar yadda sassan da suke rikici a Libya suka amince cikin makon jiya, daga nan yayi kira ga dokacin kasashe dake majalisar, su bada cikakken goyon baya ga daidaiton.

Kudurin haka da Birtaniya ta gabatar, yayi kira ga majalisar shugaban kasa a Libyan ya aiwatar shirye shiryen kafa sabuwar gwamnati cikin kwanaki 30, tareda daukar matakai na tsaron kasar.

Jakadan Libya a Majalisar Dinkin Duniya, Ibrahim Dabbashi, ya gayawa kamfanin dillancin labarai na AssociatedPress cewa, yana fatar ganin MajalisarDinkin Duniya ta sassauta takunkumin da ta aza na hana sayarwa kasar makamai, domin kasarta kare kanta daga kungiyar ISIS, wanda zai kawar da bukatar kasashen yammacin duniya su taimak tare da jiragen yaki.

Kwamitin sulhun, ya kuma yi Allah wadai kan duk wani nau'i na ta'addanci a Libya da ISIS tareda magoya bayanta suke kaiwa a Libya, hakan nan kwamitin ya bayyana damuwa kan tabarbarewar rayuwa a kasar.