Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Libya: Bangarorin dake Adawa da Juna Sun Cimma Wata Yarjejeniya


Binkin sanya hannu kan yarjejeniyar da bangarorin suka cimma
Binkin sanya hannu kan yarjejeniyar da bangarorin suka cimma

Bangarorin da ke takaddama da juna a kasar Libya, sun cimma wata yarjejeniyar kawo karshen rikicin siyasar da ya addabi kasar na tsawon shekaru da dama.

Idan kuma har majalisar dokokin kasar da kasashen duniya suka da ita, ta yi na’ama da wannan matsaya da aka cimma a jiya Lahadi a Tunusia, ana sa ran za a kawo karshen rikicin da ya barke a kasar tun bayan hambarar da gwamnatin Moammar Ghaddafi.

A cewar mataimakin shugaban majalisar kasar da ke birnin Tripoli, wato Mohammed Awad Abdul Sadiq, wannan rana ce da mutanen kasar Libya da larabawa da ma duniya baki daya suka dade suna jira su gani.

Tun dai bayan da suka sha kayi a zaben da aka gudanar a bara, mayakan sa-kai da ke goyon bayan jam’iyyun Islama da dama, suka karbe ikon babban birnin kasar da sauran ma’aikatu, lamarin da ya tilastawa majalisar wakilai da sauran jami’an kasar ficewa zuwa Tobruk da ke gabashin kasar domin gudanar da ayyukansu.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG