Mazauna Kusa Da Iyakokin Nijar Suna Zaman Dardar Sakamakon Cikar Wa’adin ECOWAS

Mazauna Iyakar Najeriya da Nijar na ci gaba da rayuwarsu ta yau da kullum

‘Yan Najeriya mazauna yankunan da ke daura da iyakokin Jamhuriyar Nijar na ci gaba da zaman rashin tabbas kan abin da ka iya biyo bayan wa'adin da kungiyar ECOWAS ta bayar ga gwamnatin mulkin soji da suka hambarar da gwamnatin farar hula a kasar.

SOKOTO, NIGERIA - Iyakokin Najeriya da Jamhuriyar Nijar sun kasance wuraren da koda yaushe ke cikin hada-hadar kasuwanci da cudanya tsakanin al'ummomin kasashen biyu.

Garin Ilela akan Iyakar Najeriya da Nijar

Duk da kasancewar wa'adin da Kungiyar ECOWAS ta bayar ga jagororin Gwamnatin soji da ke rike da iko a Nijar ya kare ranar Lahadi, jama'a a bakin iyakar kasashen biyu dake garin Illela ta jihar Sakkwato da ke Arewa maso Yammacin Najeriya sun ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum, duk kuma da yake suna cikin rashin tabbas kan abinda ka iya faruwa na amfani da karfin Soji a Nijar.

Wasu mazauna garin Illela da suka zanta da Muryar Amurka sun bayyana cewa da farko sun kasance cikin fargaba amma daga baya da wa'adin da ECOWAS ta bayar ya cika ba a yi komai ba, hankalinsu ya kwanta kuma sun ci gaba da lamurransu na yau da kullum.

Wasu kuma sun nuna bacin rai akan yadda yanzu idan ‘dan Najeriya ya shiga Nijar mutanen kasar ke yi masa wulakanci.

Mazauna Ilela a Iyakar Najeriya da Nijar na ci gaba da rayuwarsu ta yau da kullum

Mukhtar Tukur Abdulrahman Ciroman a Illela ya ce a halin yanzu jama'ar garin na zaune lafiya suna ci gaba da lamuransu na yau da kullum.

Bakin iyakar kasashen biyu ya kasance a rufe, sai dai rufe iyakar bai hana shigowa ko fitar mutane ba, ta amfani da hanyoyin kasa dake cikin dazuka, har mun samu kokarin zantawa da wasu ‘yan Nijar wadanda suka tabbatar mana cewa suna shiga Illela domin sayen kayayyaki da suke bukata.

Kasancewar yankin bakin iyakar Najeriya da Nijar akwai jami'an tsaro masu yawa daga hukumomin Gwamnati wadanda ke aiki a yankin , sai dai daga baya an tabbatar da shigowar karin wasu Sojoji a garin tun kafin a yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar, sai da Abubakar Jarman wani mazaunin Illela ya ce da ma an tura su Illela ne saboda matsalar rashin tsaro da ta addabi yankin.

A halin yanzu dai al'amura na gudana ba wani sauyi a garin na Illela da ke jihar Sakkwato garin da ya yi iyaka da Jamhuriyar Nijar.

Saurari cikakken rahoto daga Muhammad Nasir:

Your browser doesn’t support HTML5

Mazauna Kusa Da Iyakokin Nijar Suna Zaman Dardar Sakamakon Cikar Wa’adin ECOWAS.MP3