Mazauna Abuja Na Dakon Sakamakon Zaben Shugaban Kasa 

Mazauna Birnin Abuja Na Zaman Dokin Jiran Sakamakon Zaben Shugaban Kasa

Jama’a masu zaman jiran sakamakon zaben da aka gudanar ne jiya Asabar 25 ga Fabrairun 2023.

ABUJA, NIGERIA - Wakilin Muryar Amurka da ya zagaya wasu unguwanni a yankunan kananan hukumomin Bwari, Gwagwalada da birnin na Abuja, ya iske mutane a würaren hira suna tattaunawa game da yadda zaben ya gudana tare da fatan samun nasarar zaben.

Mazauna Birnin Abuja Na Zaman Dokin Jiran Sakamakon Zaben Shugaban Kasa

Alhassan Abdulrazak da ke yankin karamar hukumar Bwari ya ce ya gamsu da yadda zaben ya kasance tare da addu’ar samun shugabannin da za su gyara yanayin tattalin arziki da zamantakewa a kasar.

Yayin da Joshua James Philips na birnin Abuja ke cewa tun jiya ya ke gaban akwatin talbijin dinsa, inda ya ke kallon yadda zaben ke kasancewa da ma abubuwan da suka biyo baya.

Mazauna Birnin Abuja Na Zaman Dokin Jiran Sakamakon Zaben Shugaban Kasa

Zaben dai da ya fi jan hankali a birnin Abuja, musamman a fafatawar da aka yi tsakanin ‘dan majalisa mai ci Philip Tanimu Aduda na Jam’iyyar PDP da kuma Alhaji Zakari Angulu Dobi na Jam’iyyar APC, wadanda dukkanninsu tsoffin ‘yan majalisar wakilan Tarayya ne, dake da gogewa a siyasar babban birnin na Tarayya da kuma suke da magoya baya daidai gwargwado.