Wasu mazabu sun kai har cikin dare ba a gama kada kuri’a ba saboda yawan jama’a, a wasu kuma saboda tsananin karancin jama’a tun kafin ma lokacin rufe rumfunan zabe suka dade da kammala nasu.
A zaben 2023, mata da yawa sun fita kada kuru'unsu, dalilinsu kuwa shi ne ba za a barsu a baya ba musamman a lokacin da Najeriya ke kokarin samun jagororin da zasu fidda kasar daga kangen talauci, da koma bayan tattalin arziki, da sauransu.
Kashi 75 cikin 100 na masu kada kuri'a a Najeriya dai mata ne da matasa a cewar wasu alkaluman hukumar INEC a baya.
Wata mata mai suna Amina Musa, ta ce ko da za ta kai sha biyun dare za ta jira har sai an kammala kidaya a rumfar zabenta. Ta kuma yi fatan Allah ya yi wa Najeriya canji da abinda ya fi alkhairi.
Ita kuma Hanifa Suleiman, wacce ta dade kan layi tana jira ta kada kuri'a, cewa ta yi mata a matsayinsu na iyaye suna dagewa ne don su karfafa gwiwa akan batun zabe. Ta kuma yi fatan wanda zai lashe zaben ya zama shugaba na gari ya kuma taimaka wa mata da sauran jama'a ta bangaren kiwon lafiya, makaranta, da tsaro.
Saurari rahoton Hauwa Umar: