Mayakan Kurdawa Da Amurka Ke Marawa Baya Zasu Fice Daga Sansanin Su

Mayakan Kurdawa da Amurka ke marawa baya sun ce zasu fice daga sansaninsu dake Gabashin kogin (Yufrats) Euphrates, rana ‘daya bayan da mayakan Turkiyya da kawayenta suka gudanar da wani hari a tsalleken iyaka.

Mayakan Kurdawa dai sun zamo makasudin zaman ‘dar ‘dar da ake tsakanin Amurka da ke ganinsu a matsayin abokan hadin gwiwa, da ita kuma Turkiyya wacce ke kallonsu a matsayin ‘yan ta’adda, wadanda ke hada kai da kungiyoyin tsirarun kurdawa dake Turkiyya.

Mai magana da yawun tawagar da Amurka ke jagoranta a yakin Syria, yace Kurdawa sun koma gabas ne domin shirin samun ‘yanci a Raqqa. Sai dai kuma babu tabbacin ko mayakan Kurdawan sun fice ne a dalilin Turkiyya ta ci gaba da kai hari.

Shugaban kungiyar Birtaniyar nan dake kula da kare hakkin bil Adama a Syria, Rami Abdel Rahman, ya fadawa kafar yada labarai ta Larabawa cewa har yanzu mayakan Kurdawa na ci gaba da fada a yammacin kogin (Yufrats) Euphrates, yanzu haka ma sun karbe ikon wasu gurare.

Ministan harkokin wajen Turkiyya yace yayi magana da sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, ta wayar tarho da safiyar jiya Alhamis, kuma yace mayakan Kurdawa zasu janye daga fadan. Mataimakin shugaban Amurka Joe Biden, ya fadawa shugabannin Turkiyya cewa Kurdawa zasu rasa goyon bayan Amurka idan har ba su koma bayan kogin Euphrates ba.