Wani rahoton asiri da aka jima ana shiryawa ya nuna cewa gwamnatin Syria da kungiyar ‘yantawayen kasar duk sunyi anfani da makamai masu guba a shekarun 2014 da 2015 a yakin da suke da junansu, abinda kuma ya saba wa Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya da ta haramta anfani da irin wadanan makaman.
Binciken fiye da shekara daya da MDD tareda wata cibiyar hankoron hana anfani da irin wadanan makaman suka gudanar, ya nuna cewa har sau biyu sojan gwamnatin kasar ta Sham suna kai hare-hare da makamai masu gubar gas na “toxic” mai sa a shake, yayinda mayakan IS kuma sau daya suka yi anfani da makamai mai gubar “mustard” watau gubar “ridi” wajen kai nasu farmakin.
A ran 30 ga watan nan na Agusta ake sa ran Kwamitin Tsaron MDD mai kasashe 15 a cikinsa zai zauna ya tattauna akan wannan lamarin, abinda ake jin zai janyo cece-kuce a tsakanin manyan kasashen nan guda biyar dake da kujerar dindindin a kan kwamitin tsaron, watau China, Rasha, Amurka, Ingila da Faransa.