Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Pakistan Ta Bukaci Burtaniya Ta Dau Mataki Kan Jagoran Kungiyar Siyasa Mai Gudun Hijira A Kasar


Kasar Pakistan ta ce ta bukaci kasar Burtaniya a hukumance, da ta dau mataki kan jagoran wata kungiyar siyasar Pakistan wanda ke gudun hijira a Burtaniyar, saboda haddasa mummunan tashin hankalin da ya faru wannan satin a Karachi.

Mutumin da ake magana akansa shi ne Altaf Hussain, wani dadadden dan ta Burtniya, wanda ke jagorantar jam'iyyarsa ta Muttahida Quami, ko MQM a takaice, daga birnin London tun bayan da ya tsere daga kasar ta Pakistan shekaru 24 da su ka gabata.

Ranar Litini, wasu mambobin MQM sun je sun yi cin mutunci a ofisoshin wasu gidajen talabijin uku da ke birnin sannan su ka fafata da 'yan sanda jim kadan bayan da Hussain ya kammala yin jawabinsa ta waya daga birnin London, wanda aka yada ta wajen amfani da 'laspika'.' Hussain ya umurci magoya bayansa su yi mummunar zanga-zangar, sannan ya ce 'tir da Pakistan.' Harin ya yi sanadin mutuwar akalla mutum guda tare da raunata wasu 7, ciki har da wani dan jarida da jami'in tsaro.

Hukumomi sun yi tir da jawabin na Hussain, wanda su ka bayyana da "jawabin tsanar kasa" sannan ta gaggauta kama shugabannin jam'iyyar da ma'aikata saboda zarginsu da taka rawa a tashin hankalin. Wasu kungiyoyin tsaro na farar hula sun kai samame a ofisoshin jam'iyyar ta MQM su ka kuma rufe su a fadin birnin da wasu manyan garuruwan da ke lardin Sindh, wanda Karachi ne hedikwatar.

XS
SM
MD
LG