Daman dai wadanan mayakan na Kurdawa sun zama wani tarnaki a dangatakar dake tsakanin Amurka da Turkiya, da yake Amurka na yi musu kallon kamar kawayenta ne, Turkiyya kuma na musu daukar ‘yan ta’adda dake da alaka da kungiyoyin Kurdawa na kasar ta.
Wani mai magana da yawun kasashen dake kawance da Amurka yace mayakan Kurdawan sun tashi ne kawai don suje su “daura damaran ‘yantar da Raqqa.” Sai dai kuma ba ma tabbas na ko idan dukkan mayakan Kurdawan ne suka tashi daga inda suke, kamar yadda Turkiyya ta nema.
Ministan harakokin wajen Turkiyya yace sunyi mjagana da takwaransa na Amurka John Kerry akan maganar janyewar mayakan Kurdawan lokacinda Kerry din yaje Saudi Arabia don zantawa da shugabannin kasashen Larabawa kan rawar soja da da Amurka ke takawa a Syria.