Rahotanni daga jihar ta Yobe dai sun yi nuni da cewa wasu da ake zargin mayakan kungiyar Boko Haram ne sun kai hari a garin Babban Gida, shelkwatar karamar hukumar mulkin Tarmuwa da yammacin ranar lahadi.
To sai dai rundunar sojin saman Najeriya da ke jihar sun sami nasarar fatattakar makaran cikin daji.
Mai taimakawa shugaban karamar hukumar Tarmuwa kan harkokin yada labarai, Bulama Jalaludeen, ya tabbatar da afkuwar lamarin ta wayar tarho da safiyar yau Litinin.
Wasu majiyoyi daga yankin kuma sun yi nuni da cewa dakarun soji da ke yankin sun sami kiran gaggawa daga bisani suka kai dauki, inda suka yi musayar wuta da mayakan har suka arce daga yankin, lamarin da ya tilastawa akasarin mazauna yankin fantsama cikin dazuka don tsira da rayukansu.
A cewar Jalaludeen, mayakan sun yi ta harbe-harben bindiga kafin dakarun soji suka iso garin tare da fatattakarsu.
Wannan harin dai na zuwa ne bayan samun dan sassauci a hare-haren da 'yan kungiyar ta Boko Haram da na ISWAP da ke mubaya’a ga ISIS ke kaiwa musamman a yankin Arewa maso gabas.
Idan ana iya tunawa a ranar 16 ga watan Satumban nan da mu ke ciki ne rundunar sojin saman Najeriya ta ce bisa kuskure wani jirgin yakinta ya bude wuta akan wasu fararen hula a kauyen Buhari da ke jihar Yobe a Arewa maso gabashin kasar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutane 8 da jikatta wasu da dama.