Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalilin Da Ya Sa Gwamnati Ta Ki Bayyana Masu Taimakawa Ta'addanci A Najeriya - Malami


Boko Haram ta yi ikirarin kakkabo jirgin saman soji.
Boko Haram ta yi ikirarin kakkabo jirgin saman soji.

Malami ya ce a halin da ake ciki na gudanar bincike, zai iya kasancewa riga malam masallaci a bayyana sunayen wadanda ake zargi, wanda kuma kan iya wargaza nasarar da ake ta samu a halin yanzu a haujin yaki da kalubalen tsaro a kasar.

Tun lokacin da gwamnatin Najeriya ta yi ikirarin cewa ta sami gano wadanda ke daukar nauyin kungiyar ‘yan ta’adda ta Boko Haram, ‘yan kasar suka kosa su ji sunayen su, da kuma matakin da gwamnatin ta ke dauka domin hukunta su.

Hakan ko ya biyo ne bayan da wasu masu fashin baki kan lamurran tsaro da dama, suka yi zargin cewa wasu manyan mutane a Najeriya ne ke daukar nauyin ‘yan ta’adda, ciki ko har da wasu manyan jami’ai da ke cikin gwamnati.

To sai dai kuma Ministan shari’a Abubakar Malami, ya ce duk da yake jama’a sun kosa da su ji ko su wanene, gwamnati ba za ta bayyana sunayen su a yanzu ba, domin kuwa yin hakan kan iya kawo cikas kan bincike da ake yi kan lamarin.

A yayin wata tattaunawa da manema labarai a birnin New York na kasar Amurka, bayan gabatar da jawabi a taron Majalisar Dinkin Duniya, minista Malami ya kara jaddada cewa hakika gwamnati ta gano wasu manyan mutane a kasar da ke taimakawa ayukan ta’addanci, kuma tuni ta soma kama wasunsu.

Ya kara da cewa “mun kuma sami nasarar toshe kafafen da ake tura kudade ga ‘yan ta’adda, yayin da kuma muka shiga gudanar da kwakkwaran bincike, wanda kuma yanzu haka yake yin tasiri sosai a yaki da ta’addanci.”

Abubakar Malami
Abubakar Malami

Malami ya ce a halin da ake ciki na gudanar bincike, zai iya kasancewa riga malam masallaci a bayyana sunayen wadanda ake zargi, wanda kuma kan iya wargaza nasarar da ake ta samu a halin yanzu a haujin yaki da kalubalen tsaro a kasar.

Akan haka ya roki ‘yan Najeriya da su kara hakuri, su bar doka ta yi aikinta, kuma ba da jimawa za su ji sunayen masu daukar nauyin ‘yan ta’adda, idan aka kammala binciken shari’a kan lamarin.

Kungiyar Boko Haram ta kwashe tsawon shekaru 12 tana ayukan kai hare-hare a yankin Arewa maso gabashin Najeriya, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutuwar dubban mutane, tare kuma raba miliyoyin iyalai da gidajensu.

XS
SM
MD
LG