Mawaki Hammudi Bin Ali Yace Yayi Waka Akan Shafe Shafe

Hammudi Bin Ali

Muhammad Aliyu wanda aka fi sani da Hammudi Bin Ali, yace yakan duba abubuwan da ke ciwa alumma tuwo a kwarya domin ya fadakar, da kuma yin nasiha a kansu a fannin sa na waka. Ya kuma ce, "a missali nakan yi waka akan matar uba, yadda wasu matan ke muzgunawa ‘ya’yan mazajensu, da iyayensu suka rasu ko ba sa gidan ta hanyar cin zarafin su.

A duk lokacin da Muhammad ya fitar da waka, yakan ji dadi idan wakar ta isa inda yake so ta kai sannan Hammudi ya ce cikin wakokin da yayi akwai wata waka da yayi wadda take yin fadakarwa akan illar shafe-shafe wato ‘Bleaching’ da nuna kyama ga wannan dabi’ar da mafi akasarin ‘yan mata keyi a wannan zamanin.

Ku Duba Wannan Ma Rawar Da 'Yan-Najeriya Ke Takawa A Duniya Ba'a Cewa Komai

Bana fuskantar matsala daga fannin iyaye na domin sun karbi sana’ar tawa da kyaukkyawar fahimta, ya kuma ce ya jima a duniyar waka. Baya ga wakokin fadakarwa yana kuma wakokin siyasa da kuma na biki.

"Na fara waka ne da wata wakar biki daga bisani na fara wakokin siyasa da kuma fadakarwa. Babban burinsa kamar kowane mawaki shine yayi fice kuma wakarsa ta yi tasiri ga alumma ba tare da ya batawa wani rai ba, a hannu guda kuma ya isar da sakonsa.

Your browser doesn’t support HTML5

Mawaki Hammudi Bin Ali Yace Yayi Waka Akan Shafe Shafe 2'20"