A yanzu muna kokarin wayar da kan matasa illar shan kwaya, amma babban matsalar dai itace, kamar yadda ake cewa idan danbu yayi yawa, baya jin mai. ganin cewar 'yan siyasa na amfani da yanayin talauci da kuma jahilci wajen amfani da matasa a matsayin 'yan bangar siyasa a cewar Abubakar Sadiq Umar.
Duk da yunkurin wayar da kan matasa illolin bangar siyasa da shaye-shaye da ake yi, na tafiyar hawainiya ne domin bita da wayar da kansu na kasancewa tamkar ana yi musu romon baka ne, maimakon a biya musu bukatunsu, sai a dinga basu kwayoyi su sha hankalinsu ya gushe.
Malam Abubakar, ya ce suna kalubalantar al'umma da masu mulki dangane da matsalolin shan kwaya domin gwamnati ke da alhaklin hana matasa shan ta, sannan a mafi yawan lokuta ko an kama 'yan kwaya amma sai masu rike da madafun iko dake amfani dasu su sa a sake su.
Su kuma matasa a hannu guda, rashin sanin ciwon kansu da maida hankali wajen samawa kasarsu cigaba ne ya haddasa wannan matsalar ta shan kwaya, duk dai da cewar talauci da matasan ke fama da shi na daya daga cikin abubuwan da suke alakantawa da wannan matsalar.
Facebook Forum