Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Aikin Jarida Shi Ne Ginshikin Zaman Lafiya A Duniya - Makanjuola


Moji Makanjuola
Moji Makanjuola

Moji Makanjuola – tun da na taso na kasance mai yawan karance-karance da son sanin tarihi, ko a makaranta abin da na fi so kenan hakan ce ta sa har na fara shawa’awar aikin jarida.

Moji ta kasance da iyayenta suka lura da yadda take son karance-karance sun kuma ba ta goyon baya dari bisa dari.

Kuma har kawo yanzu da ta daina aikin jarida a cewarta, akwai wasu rahotanin da take alfahari da su da ya shafi mata da lafiya.

Daga cikin wasu muhimman abubuwa da wasu lokutan 'yan jarida kan tsinci kansu a halin ha’ula’i na hada rahoto kamar sauran 'yan jaridan, akwai lokacin da aka taba kawo mata kudi domin ta ki amincewa ta yi wani rahoto da zai fito da rashin kyautatawa da wani kamfani ke yi.

Mun kuma tambaye ta yaya dan jarida zai bambance kansa daga hulda ta jikia da 'yan siyasa? Alal misali sanin duk wani mai kallon tashar NTA a wancan lokaci an tsinkaye ta tana yawan mu’amala da mai dakin shugaban kasa a wancan lokaci wato Mrs. Patience Jonathan, inda ta tabbata ba ta nuna bangaranci ba kamar yadda take fadi.

Daga karshe ta shawarci 'yan jarida da su jajirce wajen yin gaskiya da kauracewa bangaranci a yayin gabatar da rahotonsu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:11:08 0:00

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG