Suleiman Usman Suleiman, matashi ne dake zurfafa binciken shi a fannin kimiyya da fasaha a masana'antar islar Gas, a wata jami'ar kasar Ingila. Matakin da yake a yanzu ya bude masa ido wajen ganin halin da duniya ke ciki.
Idan akayi la'akari da irin rawar da matasan kasashen da suka cigaba suke takawa za'a ga cewar suna bada gudunmawa wajen ganin kasarsu, da tattalin arzikinta ya bunkasa.
Suleiman na ganin cewar idan har matasan kasarsa Najeriya zasu tashi tsaye haikan wajen neman hanyoyin dogaro da kai, to babu shakka, kasar zata cigaba fiye da sauran kasashe dake ikirarin cigaba.
Yana da yakinin cewa matasan Najeriya dake karatu a kasashen duniya na taka muhimmiyar rawa wajen habbakar kasashen, domin kuwa ana basu damar da ta kamata wajen baje kolin basirorisu.
Facebook Forum