Masu fashin bakin sun bayyana cewa, Shugaba Biden ya cancanci jinjina saboda abinda suka kira halin dattakon da ya nuna a wannan lamari, yayinda suka nuna gamsuwa da goyon bayan da ya baiwa mataimakiyarsa Kamala Haris a matsayin wace za ta maye gurbinsa a fafatawar da ake ganin za ta kasance mai matukar daukan hankulan kasashen duniya.
Matakin janyewar Shugaba Joe Biden daga jerin wadanda zasu kara a wannan zabe tamkar amsa ce ga wasu jiga jigan jam’iyar Democrat da ke hasashen ba zai kai labari ba a zaben mai zuwa bisa dalilai masu nasaba da yawancin shekaru.
Mai sharhi kan al’amuran yau da kullum Abdourahamane Alkassoum na cewa Biden ya yi rawar gani. Ya bayyana cewa, wannan wani salo ne irin na gogaggen dan siyasar da ya san ta inda ya kamata a bullowa kowane irin lamari saboda haka janyewarsa tamkar kara jan damara ne a wannan lokaci da siyasar Amurka ke kara zafafa biyo bayan abinda ya faru da Donald Trump inji kwararre kan huldar kasa da kasa Moustapha Abdoulaye.
Tuni hankula suka karkata wajen ganin yadda za ta kaya bayan da Shugaba Biden ya bayyana goyon baya ga mataimakiyar Shugaban kasa Kamala Harris a matsyin wace yake fatan ta tsayawa jam’iyar Democrate mace bakar fata ta farko da za ta nemi haye irin wannan tsani a tarihin Amurka.
A watan Agustan nan ne taron jami’iyar Democrate zai yanke shawara kan abinda zai biyo bayan janyewar Joe Biden wato ko su yi na’am da zabinsa ko akasin haka.
Tuni a bangaren jam’iyar Republican ta tsohon shugaban kasa Donald Trump aka fara nuna bukatar ganin shugaba Joe Biden ya yi murabus daga mukaminsa saboda yadda suke kallon matakin janyewarsa tamkar wata gazawa ce, yayinda masana kimiyar siyasa ke cewa wannan dambarwa ta siyasar Amurka na tattare da dimbin darussa da ‘yan siyasar Afrika zasu koya.
Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5