A daidai lokacin da takkadama tsakanin bangaren zartarwa da na majalisar dokokin Najeriya ke neman sauya salo, ’yan majalisar dattawa sun yanke kauna akan manyan hafsoshin tsaron kasar sakamakon abin da suka kira kasawar su wajen tsaron ‘yan kasa.
Lamarin dai ya kara kamari biyo bayan sace yara ‘yan makarantan sakandare a Kankara ta jihar Katsina da mayakan boko haram suka dauki alhaki.
’Yan majalisar dattawan Najeriya sun kara jadada matsayinsu na cewa wajibi ne gwamnatin tarayya ta saurari al’ummar kasar, ta bangaren sauya hafsoshin tsaron saboda kasawarsu wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na tsaron rayuka da dukiyoyi.
Sanata Kashim Shattima kuma tsohon gwamnan jihar Borno ya bayyana cewa duk da yake suna kaunar shugaban kasa Muhammadu Buhari, amma ba za su zura ido suna gani ana aikata ba daidai ba game da yadda gwamnatin tarayya ke ci gaba da rike manyan hafsoshin tsaro duk da cewa sun gaza wajen aikin su.
Shattima ya ce kamata ya yi a jarraba wasu manyan hafsoshi da za su ja ragamar tsaro kamar yadda shugabannin baya su ka yi.
yadda-daya-daga-cikin-daliban-da-aka-sace-a-katsina-ya-kubuta
ana-neman-hanyar-ceto-dalibai-ba-tare-da-amfani-da-karfin-soja-ba-masari
iyaye-sun-bayyana-fargabarsu-kan-garkuwa-da-daliban-najeriya
Takwarorin su na majalisar wakilai ma sun goyi bayan matakin ajiye aikin manyan hafsoshin tsaro, duk da yake an sami rarrabuwar kawuna tsakanin ‘yan majalisar wakilan daga jam’iyyun APC da PDP kan batun tsige shugaban kasa.
To sai dai mai magana da yawun shugaban kasa, Mallam Garba Shehu ya yi bayani a kan matakan da gwamnati ke dauka inda ya bukaci a ba gwamnati lokaci.
Majalisar wakilai dai ta bukaci hukumomin kasar su aiwatar da matakin gaggawa kan kare makarantu domin tsaron rayukan dalibai da malaman su daga hare-haren ‘yan ta’adda.
Saurari cikakken rahoton Halima Abdulra’uf cikin sauti
Your browser doesn’t support HTML5
Your browser doesn’t support HTML5
Your browser doesn’t support HTML5
Karin bayani akan: Boko Haram, sojoji, da jihar Katsina.