Malam Sanusi Abdul’aziz, matukin babur din adaidaita sahu ne, ya ce tun da asuba ya fita neman man fetur amma har bayan karfe 12 na ranar Talata bai san makomarsa ba, kuma bai sami damar zuwa wurin sana'arsa ba.
Shi kuwa Malam Rabi’u Yahaya, da shi ma ya yi sammakon zuwa sayen man, ya ce tun jiya yake kokarin samun man amma har yanzu bai sami hali ba.
Bayan ‘yan kasuwa da masu ababen hawa na haya, matsalar ta jefa daliban da ke zuwa makaranta cikin garari, kamar yadda Musa Habibu ya shaida.
Alhaji Mansur Tanimu, Shugaban kungiyar mammalaka da matukan baburan adaidaita sahu a Kano, ya ce lamarin ya baci, yanzu har ta kai ga wasu masu ababen hawa na adaidaita sahu na ajiye su saboda ko da sun sayi man babu riba.
Masu sharhi kan lamuran yau da kullum irinsu Kwamred Yahaya Shu’aibu Ungogo, ya ce gwamnati ce ta kyale dillalan man fetur suna cin karensu babu babbaka, amma idan gwamnati ta yi tsayin daka za a gyara lamarin.
Lokuta da yawa dai kungiyar IPMAN ta sha fadin cewa bata da iko ko zarafin yin wani abu a irin wannan yanayi, lamarin da Kwamred Ungogo ya ce ya kamata gwamnati ta tashi tsayi.
Nan take dai kungiyar IPMNAN ta jihar Kano ba ce komai ba game da batun.
Saurari rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.
Your browser doesn’t support HTML5