Daukaka karar ta biyo bayan neman takardun shari’ar da fitaccen lauyan nan mai fafatukar kare hakin bil’adama Femi Falana ya yi ranar Laraba 2 ga watan Satumba da niyar karbar aikin kare matashin.
Mai Magana da yawun kotunan jihar Kano, Baba Jibo Ibrahim ya tabbatar da mikawa lauyan takardun bayanai domin basu damar daukaka karar kafin cikar wa’adin da aka ba Yahaya Aminu Sharif ya daukaka kara, ko kuwa a aiwatar da wannan hukumcin.
“wannan kes, idan ya je kotun koli, kotun koli ta tabbatar, gwamnan Kano ba zai bata lokaci ba, zai sa hannu a kan hukumcin"
Matakin da Gwamnan Kano zai dauka
Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ce zai sanya hannu domin tabbatar da hukuncin kisan da zarar an kawo takardar teburinsa.
A jawabinsa ranar 27 ga watan Agusta, bayan sauraron jawabai daga Malamai da sauran masana shari’a da dokokin kasa, gwamnan na Kano yace, “wannan kes, idan ya je kotun koli, kotun koli ta tabbatar, gwamnan Kano ba zai bata lokaci ba, zai sa hannu a kan hukumcin. Na biyu, idan wannan wanda aka yankewa hukuncin kisa har kwanakin nan suka cika bai daukaka kara ba, to gwamnan ko minti daya ba zai kara ba, zai sa hannu domin a je a aiwatar da wannan shari’a.”
Gabanin bayyana wannan matsaya, sai da gwamnan na Kano ya gudanar da taron tuntuba da malamai, lauyoyi, shugabannin hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki, inda suka tattauna dangane da hukuncin da kotun ta yanke akan matashin.
Your browser doesn’t support HTML5
Matsayin Limaman Jihar Kano
Shugaban kungiyar limaman masallatan Juma’a na jihar Kano Sheikh Nasir Adam, ya ba gwamnan Dr. Abdullahi Umar Ganduje da gwamnatin jihar Kano shawara a zartar da hukuncin da kotu ta yanke saboda kara kare martabar addinin Musulunci.
A nashi bayanin, Malam Usman Yusuf Makwarari ya bayyana cewa, rashin zartar da irin wannan hukunci shi ke kawo tabarbarewar al’amura. Ya yi kira ga gwamnan kada ya ji tsoro ko fargaba, ya kuma bukaci a hukunta mai laifin kamar yadda addinin musulunci ya wajabta. Ya kuma ba da shawarar a zartar da hukuncin a bainar jama’a domin ya zama izina ga na baya. Sauran wadanda suka yi jawabai a zaman sun hada da Sheikh Abdullahi Pakistan wanda shi ma ya goyi bayan aiwatar da hukumcin kisan,
wata-kotu-a-kano-ta-yanke-hukuncin-kisa-kan-wani-matashi
jihar-neja-zata-amince-da-aiwatar-da-hukumcin-kisa
najeriya-ce-kan-gaba-wajen-aiwatar-da-hukumcin-kisa-a-afirka
Abinda Lauyoyi suke cewa kan hukumcin
Shugaban kungiyar lauyoyin Najeriya reshen jihar Kano Barr. Aminu Gadanya yace, kungiyar su ta gamsu da yadda alkalin kotun shari’ar musuluncin ta Kano ya yi la’akari da dokokin kasa wajen yanke hukuncin. Bisa ga cewarshi, doka ce ta kafa kotun Musuluncin saboda haka tana da hurumin yanke wannan hukumcin kan wanda ake tuhuma. Ya kara da cewa, suna bayan hukumcin da kotun da yanke dari bisa dari sabili da kotun ta bi duk ka’idojin da suka dace.
Bayanai na nuni da cewa, kungiyar lauyoyin Nigeria ta wakilta wadansu lauyoyi su binciki lamarin da nufin bin diddigin shari’ar. Kungiyar Lauyoyin ta bayyana cewa a shirye take ta kare Yahaya Sharif Aminu duk kuwa da cewa tuni babban lauya Falana ya dauke nauyin kare shi.
Wata kungiya mai hankoron kare damokaradiya CSO ta fitar da sanarwa ranar Laraba tana Allah wadai da hukumcin kisan da aka yanke wa Sharif-Aminu. Sanarwar da ke dauke da rattaba hannun sakataren kungiyar Theophilus Abu Agada, tace hukumcin ba komi ba ne face keta hakkin bil’adama da tauye ‘yancin fadin albarkacin baki.
Kungiyar ta ce ba daidai ba ne a rika kuntatawa talakawa yayinda ake kyale wadanda suke matsayin masu fada a ji da tsawatawa suna aikata manyan laifuka ana kauda kai.
Rawar da Lauya Femi Falana ya taka
Fitaccen lauya kuma dan fafatukar kare hakkin bil’adama Femi Falana ne ya shiga gaba wajen daukar matakin da ya kai ga daukaka karar ana dab da cikar wa’adin da aka dibarwa matashin kafin a aiwatar da hukumcin kisan.
Tun farko sai da babban lauyan ya yi korafin cewa sun nemi takardun hukumcin amma kotun ta Kano ta hana su, zargin da mai magana da yawun kotun ya musanta.
Mai Magana da yawun kotunan jihar Kano Baba Jibo Ibrahim ya ce Cif Falana ya nemi a bashi kofin hukumcin ne ranar Talata, kafin lauyoyin suka daukaka kara kashe garin mika masu takardun.
Bayanai na nuni da cewa, kafin shigar Falana wannan shari’ar, matashin bashi da wani lauya da ke kare shi. Wannan na daga cikin dalilan da bai iya daukaka kara ba.
An kai karar Sharif-Aminu, da ke zaune a layin Sharifai dake Kano Municipal, bayan ya fitar da wata waka ranar 28 ga watan Fabrairu, 2020, da nan da nan ta dauki hankalin mutane, aka rika yayatawa ta hanyar sadarwar WhatsApp a watan Maris, shekara ta 2020.
Bayan da aka kama shi, kotun da ta yi zama a kadaice karkashin jagorancin Khadi Aliyu Muhammad Kani, ta same shi da laifin batanci da ya sabawa dokar Shariar Musulunci ta 2000 sashe na 382 (b) aka kuma yanke mashi hukumcin kisa ta hanyar rataya. Yanzu haka Sharif-Aminu yana kulle a gidan yari inda ake tsare da shi tunda aka kama shi, yana jiran makokarshi.
Kafin kama Sharif-Aminu dai duk da yake mawaki ne, ba fitacce ba ne ko a tsakanin kungiyar mawakansu ‘yan Tijjaniya.
Hukumcin kisa nawa kotun Musulunci ta Kano ta yanke?
Ba wannan ne karon farko da kotun Musulunci ta jihar Kano ta yanke hukumcin kisa ba. A shekara ta dubu biyu da goma sha biyar, kotun Musuluncin ta yankewa wadansu mutane tara da hukumcin kisa wadanda kotun ta same su da laifi a karkashi doka ta 404 na kundin tsarin dokokin shari'ar musulunci ta shekara 2000 ta jihar Kano.
Kotun ta kuma yankewa Abdul-Aziz Dauda,wani malamin addinin musulunci sda aka fi sani da Abdul inyas, hukumcin kisa ta hanyar taraya a watan janairun shekara ta dubu biyu da goma sha shida, bayan ta same shi da laifin furta kalaman batanci ga manzon Allah.