An gabatar da mutanen a babbar kotun shari'ar musulunci da take Rijiyar Lemo cikin birnin Kano .
Cikinsu akwai wata Hajiya Mero Ibrahim da kuma wasu mutane guda goma sha biyu da laifin batanci ga manzon tsira (saw).
Bayan sauraren shaidu da kuma nazari da kotun tayi a ranar 25 ga wannan watan sai ta zartar da hukunci.
Kotun ta ce hudu gada cikin wadanda suka gurfana gabanta wato Alkasim Abubakar da Yahaya Abubakar da Isa Abubakar da Abdullahi Abubakar ta sallamesu ta kuma wankesu daga laifin da aka gabatar gabanta.
Sauran guda taran kuma kotun ta samesu da laifin a karkashi doka ta 404 na kundun tsarin dokokin shari'ar musulunci ta shekara 2000 ta jihar Kano. Dukansu an yanke masu hukuncin kisa.
Wadanda aka yankewa hukuncin kisan nada damar daukaka kara. Shari'ar musulunci ta bada damar daukaka kara. To amma doka ce ta Allah wadda ba'a iya tunbuketa.
Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.