Wani kakakin kungiyar ta Ansar Dine, ya gayawa gidan rediyon nan na Muryar Amurka cewa wannan mutumen, wanda Ba’azbine ne, an kashe shi ne ta hanyar harbe shi jiya Talata da marece a birnin Timbuktu.
Mai maganar, Sanda Ould Bouamama, yace Ansar Dine ta aiwatarda wannan hukuncin kashe mutumen ne a bisa aiki da Shari’ar Musulunci.
Boumamama yace wanda aka kashen da kansa ya akrba cewa lalle ya kashe wani mutum a kan wata rigima da ta kaure a tsakaninsu. Kuma ma shi da kansa ya kai kansa wurin hukuma.
Wannan dai shine karo na biyu da kungiyar Ansar Dine, daya daga cikin mungiyoyi ukku dake neman shimfida tsarin shari’ar Musulunci a kasar mali, take aiwatarda hukuncin kisa irin wannan a bainar jama’a.