Su dai matasan PDP sun kira gwamnatin Buhari da ta daina yin anfani da karfin tsiya wajen tozarta 'yan adawa.
To saidai kwamred Jamilu Yusuf dae jagorantar matasan dake goyon bayan APC yace sam ba haka ba ne.Yace babu alamar nuna karfin iko ko tozarta 'yan adawa a yakin cin hanci da rashawa da gwamnatin APC ta dukufa yi.
Yace akwai shaida cewa kudaden da ake bin sawunsu an samosu ne daga baitulmalin kasar. Yace hatta na hannun daman shugaba Buhari Kanar Jaafaru Isa an kama shi akan zargin karbar Nera miliyan dari daga kudaden.
Cecekucen matasan jam'iyyun ya jawo hankalin wasu 'yan siyasar kasar. Tsohon sakataren jam'iyyar Alliance for Demokracy ko AD Abdullahi Garba Muhammad yace babu yadda za'a yi wasu su wawure dukiyar kasa su bar mutane cikin talauci kuma a barsu. Yace idan ana son a kafa kasa bisa tafarkin gaskiya dole mutane su yi hakuri da abubuwan da gwamnati ke yi yanzu. Ya gargadi kowa ya bi hanyar gaskiya.
Shi Alhaji Ibrahim Aliyu Sarkin Kifi jigo a jam'iyyar PDP ta Gombe yace sun gamsu da tafiyar mulkin gwamnatin Buhari.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5