Matasan Kudancin Kaduna Sunce Shugabanninsu na Yau su Kuka da Kansu a Zaben 2015

Shugaban Najeriya

A wani taro manema labarai da matasan kudancin Kaduna suka shirya sun ce shugabanninsu kama daga shugaban kasa har 'yan wakilai basu kula da kisan killa da ake yi masu ba.
Matasan kudancin Kaduna sunce idan aka cigaba da kashesu kamar kiyashi to su da gwamnatin jam'iyya mai ci yanzu sai dai a lahira.

Wata kungiyar matasan kudancin Kaduna tace tunda 'yansiyasa daga shugaban kasa sun nuna halin ko in kula gameda halin da suke ciki to su kuka da kansu idan zabe ya zo a shekarar 2015 domin babu wani dalilin da zai sa su zabesu. Shugaban kungiyar Dr John Danfulani yace tashe-tashen hankulan dake faruwa a kundancin Kadunan sun isa haka.

Dr Danfulani yace sun kira 'yan jarida ne su gayawa duniya cewa kashe-kashe da ake yi a yankinsu ya isa kumasun gani kaman shi shugaban kasa da gwamna basu kula ba. Yace ana kashesu kamar kiyashi amma basu kula ba. Shugaban kasa bai taba magana ko ta hannun jami'in yada labaransa ba har wai a ce ya yi masu jaje. Sabili da haka suna ganin cewa ba'a daukesu tamkar mutane ba da suka san abun da suke yi. Yace suna gayawa duniya idan an cigaba da hakan to su da shi sun raba gari dangane da zaben 2015. Yace ba zasu zabi wanda zai zauna a fadar gwamnati yana shaholiya yayin da ake cigaba da kashesu. Yace sun zargi 'yan siyasa daga shugaban kasa har zuwa kansala da rashin kulawa da su.

Shugaban kungiyar yace ko sau daya babu wanda ya ambaci irin kisan gillar da ake yi masu a kudancin Kaduna. Su kam idan zabe ya zo ba zasu kai labari gida ba.

Sai dai duk da barazanar da 'yan kudancin Kadunan suka yi gwamnatin jihar tace ta riga ta tashi tsaye domin ganin an kawo karshen kashe-kashen. Kwamishanan yada labarai na jihar Mr. Ben Bako yace gwamnati zata duba rahotannin baya domin nazarin shawarwarin dake cikinsu. Yace a shekarar 2012 tsohon gwamnan jihar marigayi Parick Yakowa ya kafa wani kwamiti kan zaman lafiya. Kwamitin yayi aiki kuma ya bayarda shawarwari da majalisar dokoki ta karba domin ta yi muhawara a kai. Yanzu zasu koma ga rahoton domin su yi anfani da shawarwarin da kwamitin ya bayar. Manufa nan itace domin a inganta sasantawa tsakanin al'ummomin jihar da karfafa fahimtar juna.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Matasan Kudancin Kaduna Sunce Shugabanninsu na Yau su Kuka da Kansu a Zaben 2015 - 3'31"