Uwar jam'iyyar APC ta shigo domin dinke barakar dake akwai tsakanin jam'iyyun adawa da kuma 'yan jam'iyyar PDP da suka shiga jam'iyyar. Kwamitin sulhun yana karkashin tsohon gwamnan jihar Zamfara Ahmed Sani Yerima domin ya zauna da su ya kawo sulhu.
Alhaji Tijjani Musa Tumsa sakataren jam'iyyar na kasa ya kara haske kan batun. Yace sun yi muhawara kan al'amarin jihar Gombe. Sun gane cewa lamari ne na siyasar hadaka tunda jam'iyyu dake fafatawa da juna suka hade tare da 'ya'yan sabuwar PDP. Yace yanzu ne za'a zauna a fitar da shugabanni na ainihi da zasu rike harkokin jam'iyyar na shekara hudu.
Da aka tambayeshi ko sun zauna da bangarorin dake korafi, Alhaji Tumsa yace sun zauna dasu sun tattauna da juna. Sun yi muhawara kuma an samu hanyar da za'a cigaba da tafiya tare. Ahmed Mailantarki dan majalisar tarayya kuma jigo a jam'iyyar APC na daga cikin wadanda suka halarci taron.
Mailantarki yace uwar jam'iyyar ta dauki matsayi cewa ba zasu bari abuwa su tabarbare ba a Gombe. Dole a samu masalaha a yi gyaran da yakamata yadda jam'iyya ta tsarasu. Duk ginin da aka yi ba'a kan ka'idar jam'iyya ba za'a rushe a sake lale.
Ga karin bayyani.