Olu Falae ya yi jawabin ne a wani taron neman zaman lafiya da aka shirya. Yace ya samu sunan ne kusan shekaru 20 da suka gabata lokacin da yake neman takarar shegaban kasa a karkashin inuwar jam'iyyar SPD ta wannan lokacin. A lokacin ne ma marigayi Shehu 'Yar'adua yake nema. Olu Falae yace farin jini da yayi a arewa ya sa abokan hamayya suka ce shi arne ne kada a zabeshi.
Yayin da siyasar addinin ta kunno kai Abubakar Rimi dake mara masa baya yace iyayen shi Olu Falae hausawa ne daga Kano dake fataucin goro a Ondo. Domin haka Olun nan na nufin Auwalu haka kuma babansa Falae ai Falalu ne. Inji Abubakar Rimi sunan Olu Falae na gaskiya shi ne Auwalu Falalu daga Kano.
Kodayake abunda Abubakar Rimi ya fada ba gaskiya ba ne amma sun ji dadi kwarai. Chief Falae yace ko yau abokaina 'yan arewa suka kira ni da sunan bana kin amincewa. Irin wannan tunanen ya sa gamayar kungiyar matasan arewa suka yi taro a Abuja domin karfafa kenfen din kaucewa yin anfani da addini domin cin ribar siyasa
Hassan Waziri Cinade shugaban kungiyar yace lokaci ya yi su hadu a matsayinsu na matasan arewa babu Musulmi babu Kirista ko maganar wani yare amma kowa dan arewa ne. Su Sardauna da Abubakar Tafawa Balewa sun dauki kowa dan arewa ne domin haka matasan arewa su dunkule su zama tsintsiya madaurinki daya. Yace su zauna su ga menene matsalolin arewa kuma yaya za'a warwaresu. A nema wa matasa aikin yi a kuma wayar masu da kawunansu kan illar shaye-shye da wasu ke yi. A nemi hanyar da za'a inganta ilimi. Idan kuma ba'a yi hakan ba to abubuwan da zasu faru nan gaba sai sun fi na yanzu muni.
Wani Shehu Aliyu ya shawarci shugabannin arewa dake halartar taron kasa su bari manufofinsu su zo daya. Haka ma wani daga kabilar Igbo Mathis Igwe yace Najeriya ma ai daya ce domin akwai mutanen arewa a kudu kuma akwai mutanen kudu a arewa. Yace domin haka duk kungiyoyin da suka fito suka ce suna neman zaman lafiya a kasar suna goyon bayansu. Yace talauci da rashin aikin yi basu da addini ko kabila.
Siyasar addini da kabilanci ta kunno kai ne lokacin zaben Abiola da Kingibe a shekarar 1993 wadanda dukansu Musulmai ne. Yanzu zai zama da mamaki a samu shugaban kasa da mataimakinsa su fito daga addini daya. Yaushe Najeriya zata koma kan siyasar cancanta ba bisa ga addini ba ko kabilanci?
Ga karin bayani