NIAMEY, NIGER - A sanarwar da suka fitar wadanan matasa sun ce hada kan ‘yan kasa da samar da aikin yi ga matasa na daga cikin abubuwan da suka zama wajibi hukumomi su maida hankali kansu domin murkushe matsalar tsaron da ke kara ta’azzara a kasar.
La’akari da yadda alamomi ke nuna jan kafa ko kuma rashin bullo da wani tsarin da zai bayar da damar fara tattauna hanyoyin mayar da kasar karkashin gwamnatin dimokradiya ya sa matasan makarantar Ecole Democratique et Politique tunatar da shugabanin majalissar CNSP alwashin da suka sha a washegarin juyin mulkin 26 ga watan Yulin 2023.
A cewar matasan ci gaba mai dorewa a kowace kasa abu ne da ya danganta daga salon mulkin da ke la’akari da wasu sharuda.
Matsalolin tsaron da ke addabar kasa a sanadiyar tabarbarewar al’amura a kasashe makwabta wani abu ne da matasa masu Da’awar Bunkasa Dimokradiya da Siyasar ci gaban kasa suka ce sun yi amana za a iya shayo kansa idan ‘yan kasa suka kasance tsintsiya madaurinki daya idan kuma aka hada da saka matasa cikin kyaukyawan yanayin rayuwa.
A karshe matasan na Ecole Democratique et Politique sun yi kiran al’umma akan maganar son kasa.
Shugaban majalissar CNSP Janar Abdourahamane Tiani a jawabinsa na watan Agustan 2023 ya ayyana cewa shi da mukarrabansa ba su da niyar dawwama akan karaga, asali ma ya na fatan gudanar da al’amuran mulkin rikon kwaryar da ba zai fice shekaru uku ba.
Haka kuma a sanarwar da suka fitar a ranar 16 ga watan Maris din da ya gabata hukumomin mulkin sojan sun kara nanata wannan ikirari.
Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5