Matasan jam'iyyar APC sun shirya taron fadakarwa kan illolin siyasar banga
WASHINGTON, DC —
A siyasar banga ana yin anfani da matasa domin biyan bukatatun 'yan siyasa bayan zabe kuma a yi watsi da su kana su rikide su zama 'yan tashin hankali ga jama'a.
A wurin taron an gabatar da jawabai da kuma kasidun da suke bayani da irin dabarun da za'a bi a tsarkake siyasa. Alhaji Sani Gwamna Mayanci sakataren kudi na matasan jam'iyyar ya yi bayani kan matakan da za'a dauka domin dakile siyarsar banga.
Alhaji Mayanci yace akwai matakai da za'a dauka dangane da matasa na samar masu ayyukan yi tun daga kananan hukumomi zuwa jihohi da kuma gwamnatin tarayya gaba daya. Samar masu aiki shi zai sa a tsaftace du wasu alamura na siyasa a cikin kasar. Yace a jam'iyyarsu duk abun da za'a yi a tsarkake harakar siyasa za'a yi shi.
Alhaji Abubakar Tsafe shugaban karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara yace an yi walkiya kowa ya ga haske. Yace 'yan Najeriya sun sha azaba dalili kenan koina mutum ya je kowa na jiran ya karbi jam'iyyar APC.
Nurudeen Mohammed Badamasi shugaban jam'iyyar a jihar Bauchi yace yanzu abun da suka sa gaba shi ne wayarwa matasa kai "dalili kwa an dade ana anfani da matasa". Tun da aka fara siyasar farar hula a shekarar 1999 ana ta yin anfani da matasa amma ba'a taba samun cigaba ba. Sun kirkiro da kungiyar ne domin su ja ma matasa kunnuwa kada su kuskura su bari a yi anfani da su. Domin bayan zabe ana yin watsi da su, a barsu ba aikin yi suna shan kwaya suna kashe kansu. Matasan basu da sana'a. Karatu ma sun ki su yi.

Your browser doesn’t support HTML5