Cikin shirin matasa masu basira mun sami jin tarihin Abdulmalik Saidu Mai buredi dalibi ne wanda ya dogara da sana’ar saida buredi yan biyawa kan shi bukatu, kuma yayi almajiranci a baya.
An dai haifi matashin ne a garin Gusau, haka kuma tun yana yaro iyayensa suka tura shi almajiranci wani gari da ake kira ‘dan sadau. Alokacin ya da shekaru 6 zuwa 7, ya koma gida daga almajiranci yana da shekaru 12 a duniya, inda aka saka shi a makarantar firamare tare da koya masa yin sana’ar saida buredi.
Yanzu haka dai Abdulmalik ya kammala firamare da sakandare harma yana karatun a kwalejin horas da malamai, wanda kuma har yanzu yana wannan sana’a ta shi ta saida buredi.
Domin sauraren cikakken tarihin Abdulmalik danna nan.