Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Saboda Cutar Zika Kanfanin Tata Motors Zai Canzawa Motarsa Mai Suna Zica Suna


A yau talata ne babban kamfanin kera motocin nan na kasar India mai suna Tata Motors ya fitar da sanarwar cewa zai canza sunan daya daga cikin irin motocin da yake kerawa wadda tun daga farko yasa wa suna ZICA, a sakamakon barkewar wata sabuwar cuta mai suna irin wannan.

A kwana kwanan nan kamfanin Tata ya yi ta tallar wannan 'yar karamar mota da ya sama suna ZICA, wadda cikakken sunan ta shine "zippy car" da kamfanin ke tallatawa tare da nuna hotunan fitaccen dan wasan kwallon kafar nan na kungiyar Basalona Lionel Messi.

Lamarin ya zo ne a daidai lokacin da wata sabuwar kwayar cuta da wani irin nau'in sauro ke haddasawa mai suna irin na wannan mota ZIKA, wadda ke sa ana haihuwar yara da kananan kawuna da kuma rashin lafiyar kwakwalwa a yankin latin Amurka.

Kamfanin ya ce burinsa na kera irin wannan mota shine domin matasa kuma a shirye yake domin zuwa birnin New Delhi inda za'a nuna motar a bainar jama'a a cikin tallace tallacen sa na sabbabin motocin wannan sabuwar shekara.

Dalilin barkewar wannan annoba a kasar Brazil yasa kasar ta ja kunnen mata masu juna biyu da su kaucewa hallatar wuraren da za'a gudanar da wasannin Olympic da za'a fara a watan Agstan wannan shekarar a Rio de Janeiro.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG