Hukumar ‘yan sandan jihar Gombe ta kaddamar da bincike doming gano wadanda ke da hannu wajen mallakar takardun jefa kuri’a na jabu da aka samu wasu batagari dayin amfani dasu.
Binciken dai ya nuna wasu matasa ne suka shiga makarantar sakandaren gwamnati, ‘dauke da kamara ta ‘daukar hotan bidiyo suka kuma nemi amincewar ‘daliban makarantar da su taimaka musu don dangwala yatsunsu kan takardun jefa kuri’ar, harma sukayi wa ‘daliban tayin kudi in har sun amince, kuma zasu ‘dauke su hoton bidiyo amma ‘daliban basu yarda ba hakan yasa suka garzaya domin shaidawa hukumar makaranta.
A hirar wakilin mu Abdulwahab Muhammad da kakakin hukumar ‘yan sandan jihar Gombe DSP Faje Attajiri, yayi karin haske kan batun, inda yace, “an fara bincike kuma wadanda su gansu sun bayar da sheda, amma muna kokarin cewa duk wanda ke son tayar da zaune tsaye to ‘yan sandan Gombe zasu nemo su duk inda suke.”
Ya kuma ce hukumar ‘yan sanda suna gargadin cewa duk wanda yake ganin zai kawo rudani a jihar, to ya tabbatar da cewa doka fa zata haushi.