Shugaban bankin raya kasashen Afirka Dr. Akinwumi Adesina ya gargadi hukumomin Najeriya kan matakin da suka dauka na bari a rika shiga da abinci kasar daga kasashen ketare.
A cewar Adesina wannan mataki zai kassara fannin noman kasar.
“Sanarwar da Najeriya ta yi na bude kan iyakokinta don shiga da abinci a wani mataki na magance matsalar matsalar hauhawar farashin abinci da ake fuskanta na dan wani lokaci abin takaici ne.”
Adesina na magana ne a wani taro da mujami’ar Anglican ta shirya a Abuja kamar yadda shafin X na bankin raya kasashen Afirka AFDB ya bayyana a ranar Lahadi.
Taken taron shi ne, “tabbatar da samar da abinci da kudaden shiga a nahiyar Afirka: Rawar da Mujami’a za ta taka.”
Shugaban bankin na AFDB ya kara da cewa, “babu yadda za a yi a daidaita farashin kayan abinci ta hanyar shiga da abinci cikin Najeriya. Kamata ya yi a rika samar da karin abinci don daidata farashin, a kuma samar da abinci da takaita canja kudaden ketare, wanda hakan zai sa Naira ta samu daidaito.”
A farkon watan Yuli Ministan noman Najeriya Abubakar Kyari ya ce gwamnatin tarayya za ta cire kudaden haraji wajen shiga da masara, alkama da wasu nau’ukan hatsi tsawon kwanaki 150.
Sai dai Adesina ya ce wajibi ne kasa ta san yadda za ta iya ciyar da kanta ba tare da ta dogara da wata kasa ba idan har tana so ta yi tunkahon zama kasa mai cin gashin kai.