Matakin da babban bankin Najeriya na CBN ya dauka na zuwa ne bayan ci gaba da korafe-korafe da ‘yan Najeriya ke yi a kan yanayin matsin rayuwa da suke ciki, duk da umurnin kotun kolin kasar na cewa ‘yan kasa su ci gaba da amfani da tsoffin takardun kudi na dubu daya, da dari biyar har zuwa ranar 31 ga watan Disamban shekarar 2023.
Shin akasarin 'yan Najeriya na da masaniya a game da umurnin da bankin CBN ya bayar na bude bankunan kasuwanci a ranakun Asabar da Lahadi? Aisha Salisu Muhammad, ‘yar kasuwa ce a Najeriya kuma mai gwagwarmayar yau da kullum, tana mai cewa yawancin mutane basu san da wannan ci gaba da aka samu ba.
A wani bangare kuma, wasu masu kanana da matsakaitan sana’o’i a kasuwar Masaka da ke tsakanin birnin tarayya Abuja da jihar Nasarawa, sun ce sun fara ganin tasirin matakin a kasa.
Shi ma masanin tattalin arziki Malam Kasim Garba Kurfi, ya ce matakin bankin CBN na baya-baya na da matukar muhimmanci ga tattalin arzikin Najeriya da ke cikin matsi.
A ranar Juma’a ne dai babban bankin Najeriya ya bada umarni ga bankunan kasuwancin kasar da su bude kofofinsu don ganin an bai wa 'yan kasa damar cire kudadensu don mu’amallar yau da kullum sakamakon irin matsin da ake ciki na karanci takardun kudi a kasar.
A cikin makon da ya gabata babban bankin Najeriya ya sanar da cewa ya fitar da kudin da suka kai Naira tiriliyan daya, abinda al’ummar kasar suka ce basu gani a kasa ba.
Saurari rahoton Halima Abdulrauf:
Your browser doesn’t support HTML5