Ana sa ran Mataimakin Shugaban kasar Iran na daya Muhammad Mokhbar ya dare kan karagar mulkin kasar sakamakon rasuwar Shugaban Kasar Ebrahim Raisi a wani hadarin jirgin saman shelkwafta a daidai lokacin da kasar ke shirye-shiryen tunkarar zabubbuka nan bada jimawa ba.
Kundin tsarin mulkin Iran ya shardanta cewar "mataimakin shugaban kasar na 1 ne dare kan kujerar mulkin matukar shugaban kasar ya mutu ko aka sallame shi ko ya ajiye aiki ko ya karauce ko kuma ya kamu da wata larurar rashin lafiya tsawon fiye da watanni 2".
Raisi, wanda ya rasu a jiya Lahadi tare da Ministan Harkokin Wajen Kasar Hossein Amir Abdollahian da wasu jami'an gwamnati, na daf da kammala wa'adin mulkinsa na farko na shekaru 4 a matsayinsa na shugaban kasa.
Nadin Mokhbar na wucin gadi na bukatar samun amincewar ja goran addinin kasar Ayatollah Ali Khamenei, wanda shine kololuwa a harkar mulkin kasar.
A cewar kundin tsarin mulkin kasar, wajibi ne a gudanar da zaben da zai samar da tabbataccen wanda zai gaji kujerar shugaban kasar cikin kwanaki 50.
Wani kwamitin da zata kunshi kakakin majalisar dokokin kasar da jagoran bangaren shari'a da mataimakin shugaban kasar ne za'a dorawa alhakin shirya zabubbukan kasar.
An zabi Mokhbar mai shekaru 68, a matsayin mataimakin shugaban kasar sa'ilin da ra'isi ya karbi mulki a watan Agustar 2021.