Mataimakin Shugaban Ghana Dr. Bawumia Ya Nemi Hadin Kan Kungiyoyin Musulmai Da Sauran Addinai Don Ci Gaban Kasar

Taron Karawa Juna Sani Na Musulman Ghana

Dr. Bawumia ya bayyana hakan ne a lokacin wani taro da kungiyar Musulamai ‘yan majalisar dokokin Ghana tare da hadin gwiwar ofishin limamin limaman kasar suka shirya don hado dukkan shugabannin akidun kasar domin tattaunawa.

Yayin da yake bude taron na kara wa juna sani na Musulman Ghana na tsawon kwanaki uku da ake kira NMC a takaice, mataimakin shugaban kasar Ghana Dakta Mahamudu Bawumia, ya nemi hadin kan kungiyoyin Musulmai dabamdaban da kuma sauran addinai domin tabbatar da hadin kan Ghana da kuma aiki da gwamnati domin ci gaban kasar baki daya.

Mataimakin Shugaban Ghana Dr. Bawumia Ya Nemi Hadin Kan Kungiyoyin Musulmai Da Sauran Addinai Don Ci Gaban Kasar

Ya kuma ce a matakin gwamnati, sun yi imani idan taron Musulman na kasa ya fara aiki, zai kasance wata hanyar hadin gwiwa mai inganci wadda zata kara wa gwamnati karfin inganta rayuwar al’umar Zango da sauran wuraren da suke da karancin ababen more rayuwa a Ghana.”

Shugabannin manyan akidu a Ghana sun halarci bukin bude taron kuma dukkansu sun bayyana farin ciki a jawaban da suka gabatar.

Zaeem Harakatil Tijjaniya na Ghana, Sheikh AbdulWadudu Cissey, ya ce tun da yake manyan akidun kasar suna teburi daya, to su hadu su yi wa kasa aiki.

Mataimakin Shugaban Ghana Dr. Bawumia Ya Nemi Hadin Kan Kungiyoyin Musulmai Da Sauran Addinai Don Ci Gaban Kasar

Limamin Ahmadiya na Ghana, Sheikh Muhammad Bin Salih, ya jinjina wa wadanda suka hada wannan taron da kuma malamai da suka ajiye bambance-bambancensu suka hadu domin ci gaban al'umar Musulmai.

Babban limamin Shi’a na kasa Sheikh Abubakar Kamaludeen, ya yi jawabinsa inda ya yi kira ga ‘yan siyasa da su yi aiki saboda Allah duk da cewa jama’a na da shakku kan duk abin da suka sa hannu a ciki.

Babban limamin Ahlul Sunna wal Jama’a na Ghana Sheikh Umar Ibrahim Imam, ya ce babbar matsalar da Musulman Ghana ke fuskanta ita ce rashin rike amana da jama’a suke zargin shugabanni da yi.

Mataimakin Shugaban Ghana Dr. Bawumia Ya Nemi Hadin Kan Kungiyoyin Musulmai Da Sauran Addinai Don Ci Gaban Kasar

Babban limamin kasa Dakta Usman Nuhu Sharubutu, wanda ya rufe jawabin malaman, ya ce duk sun fadi abinda ya kamata ya fada amma yana kira ga al’umar Ghana da su dinga godiya ga Allah da ya bai wa kasar zaman lafiya, sabanin makwabtan kasashe.

Shugaban ‘yan majalisar dokokin Ghana Musulmai da ya jagoranci shirya taron, Hon. Muntaka Mubarak, ya yi kira ga wadanda zasu zauna tattaunawar da su ji tsoron Allah wajen bada gudummuwarsu, ba tare da la’akari da matsayi ko akidar da suke bi ba.

A ranar Lahadi 25 ga watan Satumba ne dai za a rufe taron.

Saurari cikakken rahoton Idris Abdallah Bako:

Your browser doesn’t support HTML5

Mataimakin Shugaban Ghana Dr. Bawumia Ya Nemi Hadin Kan Kungiyoyin Musulmai Da Kuma Sauran Addinai Don Ci Gaban Kasar