ACCRA, GHANA - Kiran nasu na zuwa ne biyo bayan an sanar da mutuwar mutum shida tare da jikkatar wasu sakamakon wasu hare haren da wasu ‘yan bindiga suka kai a yankin mai iyaka da Togo.
Mallam Uthman Muhammad Mansur babban jami'i mai wakiltan ofis din Limamin kasar a fadar Sufeto Janar din dakarun ‘yan sandan kasar, ya ce muddin ana bukatar kawo karshen wannan matsala sai an fitar da siyasa a cikinta.
Sai dai ya fara da batun harin baya-bayan nan da ya shafi wasu matafiya ciki har da wata makauniya a inda yake cewa "mutanen sun fito cikin gari za su Togo neman abin da za su ci sai aka kashe su har da makauniya da yaro. Mutanen da suka jikkata sun kai takwas.
Rikicin Bawku akwai siyasa ciki sosai amma muddin an kawar da siyasa har aka bar ma ‘yan sanda babu shakka za'a magance ta" in ji shi.
Shi kuwa Mallam Irbad Ibrahim mai sharhi bisa harkar tsaro ya ce ya kamata gwamnati ta tuntubi sarakuna da matasa tare da girke dakaru sannan ta yi kokarin nisanta matakan samar da zaman lafiya a yankin da siyasa.
Ya ce wannan ya taimaka sosai saboda anyi anfani da sarakuna wajen yin sulhu a yankin Dagbon kuma anyi nasara, don haka wannan mataki ya taimaka sosai inji shi.
Saurari rahoto daga Hamza Adam: